Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan kasashen duniya sun gabatar da manufofin kiyaye tattalin arzikinsu don tinkarar cutar COVID-19
2020-03-17 11:06:56        cri

A kwanakin baya ne, yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri a duniya ta kawo illa ga ayyukan tattalin arzikin kasashen duniya da dama, da kuma kawo mugun tasiri ga kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, wanda hakan ya kawo barazana ga makomar tattalin arzikin kasa da kasa.

Wasu bankunan tsakiya na kasashen duniya sun sanar da manufofin kudi masu sassauci, kamar rage kudin ruwa a banki da sauransu, kana kasashe masu fama da cutar sun gabatar da manufofin goyon baya a fannin kudi, don tabbatar da biyan bukatun tattalin arziki, da tinkarar kalubale, da kuma ba da rancen kudi ga iyalai da kamfanoni.

Gwamnatin kasar Italiya ta sanar da ba da kudin Euro biliyan 7 da miliyan 500, don taimakawa jama'a, da kamfanonin kasar wajen tinkarar tasirin da cutar ta kawo musu.

Gwamnatin kasar Faransa ta kara daukar matakan taimakawa kamfanonin kasar wajen tinkarar cutar, ciki har da tsawaita lokacin biyan kudin inshore, da rage haraji da sauransu.

Bankin tsakiya na kasar Koriya ta Kudu, ya sanar da rage yawan kudin ruwa a banki zuwa kashi 0.75 cikin dari, wannan ne karo na farko da kasar ta rage yawan sa kasa da kashi 1 cikin dari.(Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China