Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gudunmawar da Sin ta bayar na abin rufe fuska 300,000 sun isa Belgium
2020-03-17 10:47:34        cri

Hukumomin agajin kasar Sin sun ba da tallafin abun rufe baki da hanci kimanin dubu dari uku ga kasar Belgium domin taimakawa kasar wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma tuni tallafin ya isa kasar ta nahiyar Turai a ranar Litinin.

Tallafin wani bangare ne na alkawarin da kungiyoyin ba da agajin kasar Sin suka yi na samar da tallafin abin rufe fuska sama da miliyan biyu da kayayyakin kiwon lafiya don tallafawa kasashen Turai. Haka zalika kungiyoyin sun aika tallafin abin rufe fuska rabin miliyan ga kasar Italiya, kasar da cutar COVID-19 ta fi kamari a nahiyar Turai.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China