Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron karawa juna sani mai taken "yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi don kare hakkin dan Adam" a Geneva
2020-03-03 13:01:41        cri

Jiya Litinin, an yi taron karawa juna sani mai taken "yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi don kare hakkin bil Adama" a fadar kasa da kasa, wato palace of nations ta helkwatar MDD dake birnin Geneva. Kuma, an yi wannan taron ne a lokacin gudanar da babban taron kwamitin kare hakkin dan Adam karo na 43 na MDD.

An shirya taron karawa juna sanin ne karkashin hadin gwiwar tawagar wakilan kasar Sin dake birnin Geneva, da tawagar wakilan kasar Kamaru dake birnin Gevena, da cibiyar nazarin harkokin kare hakkin dan Adam ta kasar Sin. A yayin taron, ministan kasar Sin mai jagorantar tawagar wakilan kasar Sin dake birnin Gevena Jiang Duan, ya bayyana cewa, aikin yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi nauyi ne dake wuyan kasa da kasa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su karfafa ra'ayin su na dunkulewar kasa da kasa, da daukar matakai yadda ya kamata domin kawar da tsattsauran ra'ayi tun daga tushensa, ta yadda za a yi riga kafi da kuma cimma nasarar yaki da ta'addanci, yayin kiyaye hakkin dan Adam kamar yadda ake fata.

Mahalarta taron suna ganin cewa, kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya suna nuna bambancin ra'ayi kan batun yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, har ma sun amince da wasu ayyukan ta'addancin, lamarin da ya haifar da matsaloli ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci. Ya kamata kasashen duniya su karfafa tsarin yaki da ta'addanci da MDD ta fitar, da nuna girmamawa ga matakan da kasashen duniya suka dauka bisa halayen da suke ciki, da karfafa mu'amala da hadin gwiwarsu kan aikin yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, kana bai kamata a nemi tabbatar da moriya a lokacin da ake gudanar da wannan aiki ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China