Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta kafa kwamitin da zai taimaka wajen yaki da kaucewa biyan haraji da halasta kudin haram
2020-03-03 10:34:02        cri

Kwararru daga fadin duniya sun tattauna da kwamitin MDD da aka dorawa nauyin bayar da shawarwarin da za su gyara tsarin hada-hadar kudi dake rashin nagartattun hanyoyin magance matsalolin kaucewa biyan haraji da kwangen harajin da halasta kudin haram da kuma cin hanci.

Shugaban zauren MDD da shugaban hukumar kula da tattalin arziki da zamantakewa ta MDD ne suka kafa Kwamitin, wanda ya mayar da hankali kan tsare gaskiya a fannin hada-hadar kudi domin cimma muradun ci gaba masu dorewa.

Kwamitin ya kunshi mambobi 15 da suka hada da malamai da masu tsara manufofi da kungiyoyin al'umma da bangarori masu zaman kansu.

Ibrahim Mayaki, tsohon Firaministan Niger kuma daya daga cikin shugabannin kwamitin, ya ce kamata ya yi, a yi amfani da kudaden da ake sacewa a boye a kasashen ketare ta hanyar amfani da kamfanonin bogi da kuma kudaden da ake wawurewa kai tsaye daga asusun al'umma, wurin kawo karshen fatara da ilmantar da kowanne yaro da ginin kayayyakin more rayuwa da za su samar da ayyukan yi da kawo karshen dogaro da ake yi a kan man fetur.

Wata sanarwa da aka fitar, ta ce kwamitin zai lalubo karin matakan da gwamnatoci da cibiyoyin hada-hadar kudi ke bukata a fannonin da suka shafi kudi da tsare gaskiya wajen mallakarsu da batutuwan haraji da cin hanci da rashawa da kwace ribar da ake samu daga aikata laifuffuka da halasta kudin haram da dawo da kadarorin da aka sace. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China