Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta fitar da kudaden ayyukan gaggawa na yaki da cutar COVID-19
2020-03-03 11:13:37        cri

Ofishin ayyukan jin kai na MDD ya fitar da dala miliyan 15 daga cikin kudaden asusun ayyukan jin kai na gaggawa domin taimakawa kasashen duniya wajen ayyukan yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, kakakin MDD ya tabbatar da hakan.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya bayyana cewa, za'a yi amfani da kudaden ne wajen gudanar da ayyukan sanya ido kan hanyoyin yaduwar kwayar cutar, da gudanar da binciken cutar, da ayyukan gwaje gwajen cutar a manyan dakunan gwaje gwaje na kasashen duniya, da kuma gudanar da sauran muhimman ayyukan yaki da cutar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China