Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka: Yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 ya karu zuwa 19,101
2020-03-21 15:45:49        cri
Bisa alkaluman da jami'ar Johns Hopkins na Amurka ta gabatar, ya zuwa kusan karfe 8 na dare a jiya, bisa agogon gabashin kasar, yawan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar, ya karu zuwa 19,101, inda 244 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

Bisa la'akari da tsananin yanayin da ake ciki, majalisar gudanarwar Amurka ta sanar da cewa, an dakatar da aikin ba da izinin shiga kasar a ofisoshin jakadancin kasar dake kasashe daban daban, tun daga jiya 20 ga wata. Sai dai za a ci gaba da kula da aikin ba da izinin shiga kasar, idan ana cikin wani yanayi na gaggawa ko kuma na musamman.

A jiyan ne kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin rufe kan iyakar kasar da makwabciyarta Mexico. Haka zalika za a rufe kan iyakar kasar da Canada, inda dukkan umarnin 2 za su fara aiki da safiyar yau Asabar bisa agogon wurin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China