Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka za ta fuskanci koma bayan tattalin arziki na kaso 12 cikin dari a watanni uku masu zuwa
2020-03-20 13:06:21        cri

Babban masani mai nazarin tattalin arziki na Merril Lynch Michelle Meyer, ya yi kiyasi a jiya Alhamis cewa, tattalin arzikin Amurka zai samun koma bayan har kaso 12 cikin dari a cikin watanni uku masu zuwa, har ma wannan adadi zai kai kaso 0.8 cikin dari a duk shekara, kuma yawan mutanen da za su rasa aikin yi zai kai kimanin miliyan 3.5.

Kamfanin Moody's mai auna ingancin tattalin arziki na kasa da kasa, kuma ya nuna cewa, gwamnatin Donald Trump na shirin gabatar da matakin kara samar da kudi har dala triliyan 1, zai jefa Amurka cikin matsalar basussuka, wanda yake dabaibaye kasar matuka.

Manazarci a Moody's ya nuna cewa, gibin kasafin kudin da Amurka ke da shi a shekarar 2019 ya kai kaso 4.6 cikin dari bisa duk GDPn kasar, a bangare daya kuma, basusukan kasar na da kaso 79 cikin dari na duk GDPn, adadin da ya kai koli a cikin tarihin Amurka, tun bayan shekarar 1948. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China