Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF: saurin karuwar tattalin arzikin duniya a bana zai karu zuwa 3.3%
2020-02-20 11:20:01        cri

Asusun ba da lamuni na IMF ya bayyana a kwanan baya, cewa tattalin arzikin duniya na samun ci gaba cikin karko, kuma hadarin da ake fuskanta na raguwa, don haka aka yi kiyasin cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya zai karu zuwa kaso 3.3% a bana, wanda ya wuce adadin na shekarar 2019. Ciki kuwa, yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya da kasashen Sin da Amurka suka cimma bisa matakin farko, ta taka rawa wajen sassauta matsin lamba da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.

Baya ga haka, asusun yana ganin cewa, halin annobar cutar numfashi ta COVID-19, mai yiwuwa zai kawo tasiri ga GDPn kasar Sin na watanni uku na farkon shekarar bana, amma ba zai murkushe ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na duk shekarar 2020 ba. Haka ma tasirin da ya yi wa sauran kasashe ba zai dore ba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China