Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta karfafa matakan bincike da kandagarki kan mutanen da suka shigo kasar daga ketare
2020-03-17 19:52:06        cri
An samu rahoton wanda ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 da ya shigo kasar Sin daga ketare tun ranar 26 ga watan Fabrairu, sa'an nan, a ranar 13 ga watan Maris, karo na farko, adadin masu kamu da cutar da suka shigo kasar daga ketare ya zarce yawan sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin kasar Sin.

Jiya Litinin, akwai sabbin mutane 21 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar Sin, kuma an samu karin mutane 20 da suka shiga kasar Sin dauke da cutar, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai mutane masu dauke da cutar 143 da suka shigo kasar Sin daga ketare. Wannan ya sa, a halin yanzu, matakan kandagarki kan shigowar masu dauke da cutar daga ketare ya kasance muhimmin aiki ga kasar Sin domin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar.

Bugu da kari, a jiya Litinin, hukumar kiwon lafiyar kasar Sin ta bukaci a ci gaba da kyautata matakan bincike da kandagarki kan mutanen da suke shigowa cikin kasar daga sassa daban daban na ketare, domin hana bazuwar cutar. Haka kuma, gwamnatoci na wurare daban daban na kasar Sin sun riga sun karfafa matakan gudanar da bincike da kandagarki kan mutanen da suke shigowa kasar Sin daga ketare bisa doka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China