Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagogin maaikatan jinya 41 dake tallafawa lardin Hubei sun koma gida
2020-03-17 19:50:10        cri

Yau Talata da safe ne, motocin dake dauke da mambobi 43 na tawagar aikin ceto ta gaggawa ta lardin Shaanxi sun tashi daga birnin Wuhan don koma gida. Wannan ita ce tawagar farko dake aikin ba da taimakon jinya a birnin Wuhan da ta koma gida daga birnin.

Rahotanni na cewa, sabo da kyautatuwar yanayin da aka samu a lardin Hubei, ofishin dake kula da harkokin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 na kwamitin tsakiya ya kira wani taro a jiya Litinin cewa, bi da bi, za a janye tawagogin dake aikin ba da taimakon jinya a lardin Hubei daga wurin, bayan da suka kammala ayyukansu. Kuma bisa shirin da aka tsara, a yau Talata, tawagogi guda 43 da suka hada da ma'aikatan kiwon lafiya guda 3675 sun tashi daga lardin Hubei sun koma gidajensu. Wadannan ma'aikatan kiwon lafiya sun ba da taimakon jinya a asibitocin wucin gadi guda 14, da asibitocin kula da masu dauke da cutar COVID-19 guda 7 dake birnin Wuhan na lardin Hubei. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China