Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Najeriya: Fasahar Sin ta yakar COVID-19 za ta karfafawa Najeriya gwiwa
2020-03-20 15:18:12        cri

Kwanan baya, jadakan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya shaidawa manema labarai na CMG cewa, Sin da Najeriya na hadin kai wajen yakar cutar COVID-19, tare da daukar matakai masu amfani.

A cewarsa, matakai uku da ake dauka na kunshe da sanar da halin da Sin ke ciki, da kuma more fasahohi da dabaru, sannan kuma sun karawa Najeriya kwarin gwiwa. Ya ce dukkanin matakan na baiwa Najeriya karfi sosai, suna dakile matukar tsoro, da daukar matakai mafiya tsanani da suka wuce gona da iri.

Rahotanni sun nuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu ne aka samu mutum na farko a birnin Lagos da ke dauke da cutar, wanda shi ne na farko a yankin Afrika dake kudu da Sahara. A wannan rana kuma, ministan kiwon lafiya na kasar ya zanta da manema labarai tare da bayyana cewa, kasarsa tana kara tuntubar kasar Sin, ta kuma dauki shirin ba da jiyya da Sin ta gabatar mata. Kaza lika ya yi kira ga jama'a da kada su shiga yanayi na fargaba.

A nasa bangare kuwa, daraktan cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya wato NCDC, a matsayin masani da ya taba kai ziyarar kasar Sin, lokacin da kasar ke namijin kokarin yakar cutar, ya bayyana cewa, ya koyi abubuwa masu amfani daga kasar Sin, yana da imanin cewa, za a dakatar da yaduwar wannan mumunar cutar.

Game da ra'ayoyin bangaren Najeriya kan matakan da Sin take dauka na yakar cutar kuwa, Zhou Pingjian ya ce, cikin kalaman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jiyo shi yana ambatar kalmar "Abin misali" da za a iya koya daga bangaren Sin.

Kafofin yada labarai na Najeriya na mai da hankali sosai, kan matakan da Sin take dauka cikin wannan yaki. A bangare guda kuma, yawancin labaran da suka bayar na bisa gaskiya, sannan kuma suna darajanta matakan da Sin take dauka. A wani bangaren kuwa, masana da dama a kasar na ganin cewa, nasarorin da Sin take samu a wannan karo, na bayyana wasu muhimman abubuwa dake cikin halayen kasar Sin, wato jagorancin jam'iyyar JKS mai muhimmanci, da kuma jagoranci da matakan da shugaba Xi Jinping ya ke aiwatarwa, ciki hadda kai ziyara wurin da cutar ta fi kamari. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China