![]() |
|
2020-03-20 11:19:59 cri |
Darakta janar na hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas, Oluwafemi Oke-Osanyintolu, ya fadawa manema labarai cewa, al'ummomin unguwannin Abule-Ado da Soba su ne wadanda matsalar ta fi yiwa mummunar barna a sakamakon fashewar da ta faru ranar Lahadi.
Akwai makarantu biyar, da coci uku, da otel guda, da kuma wani babban kanti wadanda fashewar ta lalata.
Haka zalika, kimanin gine gine 170 ne suka lalace a yankin a sanadiyyar gobara da ta barke wanda fashewar ta haddasa. Sannan akwai motocin hawa 40 da wasu manyan motoci uku duka sun lalace.
Oke-Osanyintolu ya ce gwamnan jihar Legas Babajide Sanwoolu, ya ba da umarnin tsugunar da mutanen da suka rasa muhallansu a yankin Igando, dake wajen birnin Legas.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China