Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin wasu kasashe: Matakan da Sin ta dauka na yakar COVID-19 sun cancanci a yi koyi da su
2020-03-16 13:43:46        cri
A 'yan kwanakin da suka wuce, shugaban kasar Guinea Alpha Condé da shugaban kasar Nijer Mouhamadou Issoufou da shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da ma sauran wasu manyan jami'an siyasa na kasashe masu dama da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, sun jinjinawa ci gaban da kasar Sin ta samu wajen yakar cutar numfashi ta COVID-19. A ganinsu, kokarin da Sin ke yi, ya zama abun misali ga kasashe daban-daban wajen tinkarar annobar. Sun ce kasar Sin na taka muhimmiyar rawa kan tsaron kiwon lafiyar duniya baki daya, kuma suna cike da imanin cewa, kasar za ta iya cimma nasarar yaki da annobar, tare kuma da maido da bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China