Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a duniya ban da kasar Sin ya kai 72469
2020-03-16 13:13:11        cri

Kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta fitar a jiya Lahadi ta nuna cewa, ya zuwa karfe 10 safiyar wannan rana, agogon tsakiyar Turai, sabbin mutanen da suka kamu da cutar COVID 19, ya kai 10,955 a duniya ban da kasar Sin, bisa na makamacin lokaci a ranar 14 ga wata, hakan ya sa yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya ban da kasar Sin, ya kai 72,469, kuma yawan mamata ya kai 2,531.

Ya zuwa daren wannan rana, yawan kasashen Afrika da aka gano bullar cutar ya karu zuwa 26, hakan ya sa yawan mutanen da suka kamu da cutar a Afrika ya kai 280. A cikin awo'i 24 da suka gabata, Seychelles, da Equatorial guinea, da kuma Jamhuriyar Kongo, da Afrika ta tsakiya, sun sanar da gano bullar cutar a kasar a karo na farko.

Cutar ta kawo babbar illa ga gasannin wasan motsa jiki sosai a duniya, a wannan rana, an kuma sanar da soke gasanni da dama, daga cikin su kuwa hadda babban taron wasan motsa jiki na shekarar 2020 da aka sa ran aiwatar da shi a watan Afrilu mai zuwa a birnin Beijing, wanda kwanan baya aka canja wurin aiwatarwa a Lausanne na Switzerland, amma a karshe an soke shi. Ban da wannan kuma, ma'aikatan hedkwatar kwamitin shirya gasar wasan motsa jiki na Olympics ta kasa da kasa, sun fara aiki a cikin gida daga yau Litinin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China