Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: bai kamata a alakanta kwayoyin cuta da wata kabila ba
2020-03-19 16:57:37        cri
A jiya ne, shugaba mai kula da ayyukan kiwon lafiyar gaggawa na hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, Michael Ryan, ya yi bayani game da yadda shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cutar COVID-19 a matsayin cutar kasar Sin, yana mai cewa bai kamata a alakanta kwayoyin cuta da wata kabila ko wata kasa ba.

Ryan ya bayyana cewa, cututtuka basu san kasa ba, kuma ba su san launin fata da kabila ba. Ya ce an fara gano bullar cutar H1N1 a nahiyar arewacin Amurka a shekarar 2009, amma babu wanda ya kira cutar da sunan "cutar mura ta arewacin Amurka". (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China