Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta daga matakin hadarin COVID-19 a duniya zuwa mai hadari sosai
2020-02-29 17:01:04        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta daga matakin hadarin cutar COVID-19 a duniya, daga mai hadari zuwa mai hadari sosai.

Da yake jawabi a jiya, Darakta Janar na hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce kwararru masu nazarin yanayin cututtuka na hukumar, sun yi ta bibiyar yanayin cutar akai-akai, kuma a yanzu, sun daga matakain hadarin yaduwa da tasirin cutar COVID-19 zuwa mai hadari sosai a duniya.

A ranar Alhamis ne Kasashen Denmark da Estonia da Netherlands da Nijeriya suka tabbatar da samun bullar cutar a karon farko, kuma dukkansu na da alaka da kasar Italiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China