Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bukaci a dauki matakan dakile bazuwar cutar COVID-19
2020-03-08 17:11:03        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce za'a iya cimma nasarar dakile bazuwar cutar numfashi ta COVID-19 ne ta hanyar aiwatar da kwararran matakai da ayyukan shawo kan cutar yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya ya zarce 100,000.

A sanarwar da WHO ta fitar ta ce, kasar Sin da sauran kasashen duniya suna gwada cewa za'a iya dakile bazuwar cutar ta hanyar amfani da matakai na bai daya a duniya, matakan sun hada da yin bincike a tsakanin al'umma domin zakulo dukkan marasa lafiya dake dauke da cutar, da mika su cibiyoyin kiwon lafiya, da bibiyar mutanen da marasa lafiyar suka yi mu'amala da su, da kafa asibitoci da wuraren duba lafiya don kula da masu dauke da cutar, da kuma horas da jami'an kiwon lafiya.

Hukumar ta ce daukar matakan dakile cutar da hana bazuwar kwayoyin cutar zai taimaka wajen tabbatar da ingancin tsarin kiwon lafiya kuma dukkan al'umma za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana, kana masu bincike za su iya gano takamammun hanyoyin magancewa da samar da alluran riga kafin cutar.

WHO ta ce kin daukar matakan hana bazuwar cutar ba zai taba zama hanya mai dace ba ga gwamnatocin kasashe domin hakan ba kawai zai lahanta 'yan kasar ba ne har ma zai iya lahanta al'ummomin sauran kasashen duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China