Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Yawan masu dauke da COVID-19 ya karu a duniya zuwa mutum 170,000 ta kuma hallaka mutane 6,600
2020-03-17 10:40:20        cri

Ya zuwa safiyar ranar Litinin, adadin mutane da suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai mutum 167,511 a kasashe da yankuna 152, adadin da ya karu da mutum 13,903 sama da na ranar Lahadi.

Hukumar lafiya ta WHO ta ce, an samu karin wadanda suka kamu da cutar har 13,874 a wajen kasar Sin, wanda hakan ke nuna cewa, yawan sabbin wadanda suka kamu da cutar a wajen Sin ya kai 86,434, ciki hadda karin mutane 3,388 da cutar ta hallaka.

Da yake tsokaci game da halin da ake ciki, babban daraktan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce yanzu haka ana samun karin masu harbuwa, da masu rasuwa sakamakon cutar COVID-19 a karin sassan duniya daban daban, don haka ya jaddada muhimmancin yin gwaji, da kebe masu dauke da wannan cuta.

Ya ce da safiyar wannan rana, a yankunan Turai, COVID-19 ta kara fantsama, inda aka samu karin mutane 56,000 a kasashe da yankuna sama da 50.

Ya ce kasashen Turai wadanda ko wacce ke da jama'a masu dauke da cutar sama 2,000 ciki hadda Italiya, da Sifaniya, da Faransa, da Jamus da Switzerland, dukkanin su sun bayyana kamuwar kusan jimillar mutum 45,000 a ranar ta Litinin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China