![]() |
|
2020-03-10 10:14:25 cri |
Jami'in na WHO wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai na rana-rana game da yanayin cutar, ya ce hakika cutar ta harbi mutane da kasashe da dama cikin sauri, bayan da aka ba da rahoto a karshen mako cewa, sama da mutane 100,000 sun kamu da cutar a duniya baki daya, baya ga sama da kasashe da yankuna 100 da cutar ta bulla a cikinsu.
Ya ce, maganar ita ce, ba wannan cuta ce take iko da mu ba. Ya kuma bayyana cewa, muddin aka dauki managartan matakai cikin sauri, sannu a hankali za a dakile kwayar cutar da ma hana ta shafar jama'a, kuma galibin wadanda cutar ta harba za su warke. Ya buga misali da kasar Sin, inda sama da kaso 70 na mutane 80,000 da aka ba da rahoton sun harbu da cutar, sun warke har ma an sallame su daga asibiti.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China