Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun yaba da kokarin Sin a fannin yaki da COVID-19
2020-03-19 13:02:56        cri

Kasashen nahiyar Afirka, sun jinjinawa kwazon kasar Sin wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, suna masu fatan yin koyi daga dabarun da Sin ta yi amfani da su, wajen cimma makamantan nasarorin da Sin din ta samu, a gabar da cutar ke kara bazuwa a wasu sassan nahiyar.

A ranar Laraba ne aka gudanar da taro ta yanar gizo, wanda ya hallara wakilai daga Sin da na kasashen nahiyar 24, da wakilan cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka ko Afirca CDC, inda yayin taron, aka bayyana bukatar ci gaba da kokarin tallafawa Afirka game da yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Da yake tsokaci yayin taron, babban daraktan sashen Afirka a ma'aikatar harkokin wajen Sin Dai Bing, ya ce Sin na jaddada manufar yaki da wannan annoba, tare da burin yin hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa wajen yakar wannan annoba, da ba da tallafi ga karin kasashen Afirka a wannan fanni.

Bayan bitar matakan da Sin ta dauka a yakin da take yi da cutar COVID-19, taron ya tattauna muhimman batutuwa, da amsa tambayoyi, inda cibiyar CDC ta Afirka, da wakilan kasashe 24 suka gabatar da tambayoyi ga tsagin Sin, kana wakilan Sin suka yi karin haske yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China