Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Kasashen Afrika 30 sun samu rahoton bullar cutar COVID-19 kimanin 443
2020-03-19 10:47:05        cri
Cibiyar yaki da yaduwar cututtuka ta Afrika wato (Africa CDC), ta sanar cewa, ya zuwa ranar Talata an samu rahoton kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 kimanin 443 a kasashen Afrika 30, kamar yadda hukumar ta sanar a ranar Laraba.

Africa CDC, cibiyar kiwon lafiya ce ta musamman ta kungiyar tarayyar Afrika (AU), a bisa bayanai na baya bayan nan da ta fitar a ranar Laraba game da yaduwar cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ta kuma bayyana cewa an samu hasarar rayuka kimanin 10 a kasashe hudu na nahiyar Afrika.

Kasashen hudu na Afrika da aka samu mace macen dake da nasaba da cutar COVID-19 ya zuwa ranar Talatar sun hada da mutane 4 a Masar, 3 a Algeria, 2 a Morocco da kuma Sudan inda mutum guda ya mutu, a cewar Africa CDC.

Cibiyar hana yaduwar cututtukan ta Afrika ta jaddada cewa, tana cigaba da yin aiki tare da dukkan mambobin kungiyar kasashen (AU) da matsalar ta shafa don samar da dakunan gwaje gwaje, da kuma muhimman kayayyakin da ake bukata don yaki da cutar.

Kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55 ta farfado da ayyukan daukin gaggawa na cibiyar ta Africa CDC, tun bayan barkewar annobar cutar COVID-19 a ranar 27 ga watan Janairu, kuma cibiyar ta kafa wani shirin musamman na yaki da cutar tsakanin 16 ga watan Maris zuwa 15 ga watan Afrilu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China