Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwadibuwa ta samu rahoton bullar cutar COVID-19 a karon farko
2020-03-12 09:24:11        cri

Ma'aikatar kiwon lafiya da tsabtar muhalli ta kasar Kwadibuwa ta sanar a ranar Laraba cewa, an tabbatar da bullar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a karon farko a kasar.

A sanarwar da ya sanyawa hannu Dr. Eugene Aka Aouele, ministan lafiyar kasar, ya ce tuni aka garzawa da mutumin da ya kamu da cutar domin duba lafiyarsa a asibitin koyarwa na jami'ar Treichville dake Abidjan kuma yanayin lafiyarsa tana samun kyautatu yadda ya kamata.

Ministan ya baiwa jama'ar kasar tabbacin cewa ana daukar dukkan matakan da suka dace domin kula da wanda ya kamu da cutar da kuma daukar kwararan matakan dakile bazuwar annobar a kasar.

Kawo yanzu, kasashen yankin kudu da hamadar Saharar Afrika 8 ne aka samu bullar cutar numfashi ta COVID-19 da suka hada da Najeriya, Senegal, Afrika ta kudu, Togo, Kamaru, Burkina Faso da demokaradiyyar Kongo. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China