Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU na shirin zurfafa matakan yakin da COVID-19 a nahiyar Afirka
2020-03-05 10:55:56        cri

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta jaddada muhimmancin karfafa kwarewar aiki, a fannin yaki da cutar COVID-19 tsakanin kasashen nahiyar, don haka kungiyar ke ci gaba da kokarin samar da wani sahihin shiri, na dakile bazuwar cutar, yayin da bukatar karfafa shirin nahiyar na tunkarar cutar ke kara fadada.

Cikin wata sanarwa, kungiyar ta AU ta ce dukkanin wadanda ke dauke da cutar a Afirka, mutane ne da suka yi tafiya zuwa wuraren da cutar ta bazu, ko suka yi mu'amala da masu dauke da ita, amma babu rahotannin yaduwar cutar daga mutum zuwa mutum, ko yaduwar cutar cikin gaggawa.

Hakan dai na kunshe cikin ka'idojin lura da yaduwar wannan cuta da kungiyar ta fitar, da matakan kula da tafiye tafiye da ta fitar a jiya Laraba. AU ta kuma jaddada cewa, kawo yanzu, daruruwan jami'ai daga kasashe mambobin kungiyar sama da 30, sun samu horo na aiki a dakunan gwaji, da gwaji a kan iyakokin kasashe, da aikin kandagarki da shawo kan cutar, da musayar bayanai game da hasashen yaduwar ta, da ma karin dabarun shawo kan cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China