![]() |
|
2020-03-15 16:08:43 cri |
A ranar 12 ga wata, kwararren dan jarida, kana shugaban cibiyar kafofin yada labarai ta Sin dake Afirka Ikenna Emewu ya gabatar da sharhi mai taken "Kasar Sin ta baiwa kasa da kasa tabbacin yaki da cutar numfashi ta COVID-19" a shafin intanet na cibiyarsa, inda ya nuna yabo matuka kan ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai a birnin Wuhan a ranar 10 ga wata domin kara fahimtar halin da birnin ke ciki, ya kuma nuna amincewa matuka kan matakan da kasar Sin ta dauka wajen dakile yaduwar cutar.
Cikin sharhin ya ce, ziyarar ta shugaba Xi Jinping ya kai a birnin Wuhan ta kara karfi da aniyar masu aikin ceto, lamarin da ya nuna cewa, ana dab da lokacin cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin baki daya, a sa'i daya kuma, ya baiwa kasashen duniya dake fama da cutar tabbaci na cimma nasarar yaki da annobar.
Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa da sauri cikin kasashen duniya, duk da kasancewar kasar Sin tana fuskantar irin wannan matsala, amma ba ta daina bada taimako ga sauran kasashe ba, ta samar da taimakon kudi na dalar Amurka miliyan 20 ga hukumar WHO, yayin da ta aika tawagogin masu aikin jinya zuwa kasashen Italiya da Iraki da sauransu, a sa'i daya kuma, ta nuna cewa, tana son bada taimako ga kasashen Afirka, dukkanin abubuwan ta kasar Sin ta yi tana samun yabo daga jama'a.
Bugu da kari, kasar Sin ta samar da labarai game da cutar numfashi ta COVID-19 ga kasashen Nijeriya da sauransu cikin sauri, da kuma yin bayani kan matakan yaki da cutar, ta yadda kasashen Nijeriya da sauran kasashen Afirka za su yi amfani da fasahohin Sin yadda ya kamata a lokacin da suke tsara matakan yaki da cutar a kasashensu. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China