Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cutar COVID-19 ta bulla a karin kasashen kudu da hamadar Sahara
2020-03-16 10:04:27        cri

Ya zuwa jiya Lahadi, wasu karin kasashen kudu da hamadar saharar Afirka, sun tabbatar da bullar cutar numfashi ta COVID-19, duk kuwa da matakan kandagarki da kasashen Afirka ke dauka.

A karon farko, mahukuntan kasar Ghana, sun bayyana matakan takaita shiga kasar daga waje, a gabar da aka ayyana karuwar mutane 4 da suka kamu da cutar a jiya Lahadi, wanda hakan ya kawo adadin masu dauke da cutar a kasar zuwa mutum 6. Cikin matakan da aka ayyana, baya ga masu dauke da katin dan kasa na Ghana, da kuma mutanen dake da takardun izinin zama a kasar, an hana sauran mutane da suka ziyarci kasashen dake da masu dauke da cutar idan har adadin su ya kai 200 shiga kasar ta Ghana.

A nasa bangare, shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya tabbatar da kamuwar mutane 2 da wannan cuta, inda adadin masu dauke da cutar a kasar ya kai mutane 3. Tuni dai Kenyatta ya ayyana matakan kandagarki na hana yaduwar cutar ta COVID 19, ciki hadda hana shiga kasar daga dukkanin kasashen da aka samu bullar ta.

A birnin Windhoek fadar kasar Namibia ma, gwamnati ta ba da umarnin rufe wuraren shakatawa na taruwar jama'a zuwa wani lokaci a tsawon kwanaki 30, bayan da aka samu mutum 2 da cutar ta harba a ranar Asabar.

A kasar Tanzania ma, duk da ba a samu bullar cutar ba, gwamnatin kasar ta kafa asibitocin musamman guda 5, domin tunkarar kalubalen bullar cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China