Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taimakawa kasashen da abin ya shafa da kungiyoyin kasa da kasa nauyin duniya ne dake gaban Sin
2020-03-18 20:48:14        cri
Yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana dukufa wajen ganin bayan cutar numfashi ta COVID-19, a sa'i daya kuma, tana hada kai da kasashen duniya a aikin yaki da cutar, da kuma ba da taimako ga kasashen da abin ya shafa da kungiyoyin kasa da kasa gwargwadon karfinta.

Yayin manema labaran da aka yi a yau, Geng Shuang ya ce, gwamnatin kasar Sin ta riga ta samar da kayayyakin jinya ga kasashen Iran, Koriya ta Kudu, Japan da wasu kasashen duniya da ma kungiyar tarayyar kasashen Afirka, ta kuma samar da taimakon kudi na dallar Amurka miliyan 20 ga hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO. Haka zalika, ta sanar da samar da kayayyakin jinya ga kasashe da dama da suka hada da Italiya, Faransa, Spaniya, Masar, Afirka ta Kudu da Habasha da sauransu ta yadda za su iya yaki da cutar, kuma tana maraba da kasashe kawayenta, da su sayi kayayyakin jinya daga kasar Sin.

Bugu da kari, Geng Shuang ya kara da cewa, a halin yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa a sassa na duniya cikin sauri, lamarin da ya damu jama'a. Ya kamata gamayyar kasa da kasa su hanzarta daukar matakai da niyya ta bare da bata ko minti daya ba, su kuma yi aiki tare domin tsaron lafiyar jama'a a matakin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China