Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta samar da tallafi ga kasashe masu rauni a fannin kiwon lafiya
2020-02-25 21:34:51        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin za ta samar da tallafi gwargwadon karfinta, ga kasashe masu rauni a fannin kiwon lafiya, domin karfafa ikonsu na kandagarki da yaduwar cututtuka.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne a Talatar nan, yayin da aka yi masa tambaya, game da sanarwar da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya fitar ta kafar bidiyo, lokacin da yake wa taron ministocin lafiya na kasashe mambobin kungiyar AU jawabi a ranar Asabar din karshen mako.

Jami'in na Sin ya ce, duk da yanayin matsi da wasun suke ciki, kasashen Afirka sun gabatarwa Sin tallafi mai amfani kuma a kan lokaci. Ya kara da cewa, taro na 36 na manyan jami'an kungiyar AU, da ma taron majalissar wanzar da zaman lafiya da tsaro na AU, an fitar da takardun bayan zama, wadanda a ciki aka jaddada goyon baya ga kasar Sin, a yakin da take yi da cutar numfashi ta COVID-19. Jami'in ya ce taron ministocin lafiyar kasashe mambobin AUn, ya kuma jinjinawa kwazon kasar Sin, da matakan da take dauka daki daki, na yaki da wannan annoba.

Bugu da kari, jami'in ya ce kasashen Afirka na tare Sin a dukkanin lokuta masu tsanani. Wannan a cewar sa na nuni ga irin amincewar su, da manufar kafuwar al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama.

Zhao Lijian ya kara da cewa, kamar yadda yake a al'adar Sinawa, a kan ce "Yaba kyauta tukuici", don haka Sin za ta rike wannan kawancen da kuma tallafi a zuciyarta.

Daga nan sai ya alkawarta cewa, Sin za ta ci gaba da aiwatar da sakamakon da aka cimma, game da "shawarar ziri daya da hanya daya" da kuma sakamakon da aka samu, yayin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOFAC da ya gudana a birnin Beijing. Kaza lika za ta samar da tallafi gwargwadon karfin ta, ga kasashe masu rauni a fannin kiwon lafiya, domin karfafa ikon su na kandagarki, da dakile yaduwar cututtuka, da ma samar da kwarewa a fannin kiwon lafiya a matakin yankuna, da na kasa da kasa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China