Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara hada kai da kasar Iran a kokarin tinkarar cutar COVID-19
2020-03-16 19:49:18        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin tana sa ido kan yanayin tinkarar cutar COVID-19 a kasar Iran, kana za ta samar da dauki gwargwadon karfinta. Ban da haka, kasar Sin tana kira ga gamayyar kasa da kasa, da su karfafa hadin kai tare da bangaren Iran a kokarin tabbatar da tsaron harkar lafiya a duniya baki daya.

Rahotanni na cewa, a kwanakin baya shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya yi Allah wadai da kasar Amurka kan yadda matakan takunkumin da ta sanya wa Iran suke wa kasar tarnaki, musamman ma a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19. A cewar shugaban, matakan da kasar Amurka ke dauka tamkar yanke hukunci ne kan daukacin al'ummun kasar Iran. Don haka, shugaban ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su nuna adawa da matakin sanya takunkumi da kasar Amurka ke dauka, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa, don nuna goyon baya ga kasar Iran bisa kokarinta na shawo kan annobar.

A nasa bangare, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya kara da cewa, kasar Sin ta riga ta samar da wasu kayayyakin kandagarki, ciki har da na'urar gwaje-gwajen kwayoyin cuta, ga kasar Iran. Sa'an nan ta tura wasu kwararrun kiwon lafiya masu aikin sa kai zuwa kasar Iran, don taimakawa aikin dakile yaduwar cuta a can. A cewar jami'in, kasar Sin za ta ci gaba da samar da dauki ga kasar Iran, gwargwadon karfinta, kuma bisa bukatar kasar Iran. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China