Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Yadda aka dauki matakan kandagarki kan mutanen da suke shigowa kasar Sin bai saba wa doka ba
2020-03-16 19:31:20        cri
Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Litinin cewa, hukumar lafiya ta duniya WHO ta riga ta ayyana cutar COVID-19 a matsayin annobar da ta shafi daukacin duniya, lamarin da ya sanya kananan hukumomin kasar Sin fara daukar wasu matakai na bincike da kandagarki kan mutanen da suke shigowa wurare daban daban na kasar daga ketare, kamar yadda dokokin kasar suka kayyade.

Jami'in ya ce, matakan da aka dauka sun taimaka wajen dakile yaduwar cutar, musamman ma wajen hana bazuwarta zuwa kasashe daban daban. Don haka, matakan sun nuna yadda gwamnatin kasar Sin take dora muhimmanci kan tsaro da lafiyar 'yan kasar, gami da na jama'ar sauran kasashe baki daya.

A cewar jami'in Sin, ba za a nuna bambanci tsakanin 'yan kasashen waje da Sinawa ba yayin da ake daukar wadannan matakai na kandagarki. Kana hukumomin sassa daban daban za su yi kokarin biyan bukatun mutanen, wadanda za a killace su don duba lafiyar jikinsu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China