Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba za ta manta da taimakon da kasashen Afrika ke baiwa mata a wannan mawuyancin hali ba
2020-02-25 20:02:14        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa manema labarai yayin taron da aka saba yi a yau Talata cewa, kasashen Afrika sun baiwa kasar Sin taimako gwagwadon karfin su a kan lokaci. Kuma kasar Sin ba za ta manta da hakan ba, kasancewar hakan matakin dake shaida dankon zumuncin bangarorin biyu.

Zhao Lijian ya ce Sin za ta ci gaba, da tabbatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma ci gaban da aka samu karkashin taron koli na dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika, wajen baiwa wasu kasashe da ba su da cikakken karfi a fannin kiwon lafiya taimako gwargwadon karfinta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China