Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta zargi Sin da satar wani sakamakon binciken kimiyarta da wani mugun nufi
2020-02-25 20:20:57        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau Talata cewa, wasu jami'an kasar Amurka sun baza jita-jitar cewa, wai kasar Sin ta saci sakamakon binciken kimiyar kasar Amurka, suna masu fakewa da batun kiyaye tsaron kasa, domin aiwatar da mugun nufin su.

Zhao ya ce Sin na kalubalantar Amurka, da ta yi watsi da tunanin yakin cacar baka, da tunanin wariya, ko lallai sai wani bangare daya ya samu riba, kuma wani bangaren na daban tilas ya yi hasara. Kaza lika Amurka ta daidaita matsayar ta kan hadin kan kasashen biyu a fannonin kimiya da fasaha, da al'adu da dai sauransu, da daukar matakan da suka dace, dake amfani ga kara amincewa da juna, da hadin kan kasashen biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China