Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta wanke yara 223 daga zargin alaka da kungiyoyin mayaka
2020-03-05 10:17:16        cri

Asusun yara na MDD UNICEF, ya ce a kalla yara kanana 223, ciki hadda mata 10 ne suka samu 'yanci a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, bayan da hukumomi suka wanke su daga zargin alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Da yake tsokaci game da hakan, wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins, ya ce an saki yaran ne a ranar Talata, daga gidan yari dake birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar ta Borno. Cikin yaran, a cewar jami'in, hadda wadanda suka kwashe shekaru 4 zuwa 5 ba tare da an san inda suke ba, har ma iyalan su sun fitar da rai da ganin su.

Mr. Hawkins ya ce sakin yaran babban mataki ne na inganta rayuwar yaran, wanda kuma ya cancanci yabo. Ya ce za a shigar da yaran cikin shirin musamman, wanda zai ba su damar sake komawa cikin al'umma, su kuma dauki matakin sake gina rayuwar su yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China