Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar
2020-03-04 11:33:08        cri

Jiya Talata, jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya gana da ministan harkokin wajen kasar Nijeirya Geoffrey Onyeama.

A yayin ganawar ta su, Zhou Pingjian ya yi bayani kan sabbin sakamakon da kasar Sin ta samu, wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma nuna godiya ga gwamnati da al'ummomin Nijeriya, don gane da goyon bayan da suka nunawa kasar Sin.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana aiwatar da ayyukan yaki da cutar cikin yanayi mai kyau, kuma tabbas za ta cimma nasarar wannan yaki, tare da raya tattalin arzikin kasar yadda ya kamata. Kuma kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwarta da Nijeriya, kan harkokin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da sauransu.

A nasa bangare kuwa, Geoffrey Onyeama ya jinjinawa matukar babban karfin da kasar Sin ta nuna, a lokacin da take yaki da annobar, da kuma aniyarta ta yin hadin gwiwa da kasa da kasa. Ya ce, kasar Sin da Nijeriya abokan hadin gwiwa ne bisa manyan tsare-tsare, don haka ya kamata kasashen biyu su taimakawa juna, da goyon bayan juna, kuma Nijeriya tana son karfafa ma'amalar dake tsakaninta da kasar Sin, domin zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa dukkanin fannoni, yayin da ake ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China