Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kaso 80 na wasu muhimman sassan kere-kere na kamfanoni mallakin gwamnatin kasar Sin sun farfado da aiki
2020-02-18 13:51:44        cri
A wajen taron manema labarai da aka shirya yau Talata game da ayyukan ganin bayan cutar numfashi ta COVID-19, wani jami'in kwamitin sa ido kan dukiyoyin kasa na majalisar gudanarwar kasar ya bayyana cewa, sama da kaso 80 bisa dari na wasu muhimman sassan kere-kere dubu 20, na kamfanoni mallakin gwamnatin kasar sun farfado da ayyukansu.

Kwamitin zai jagoranci kamfanoni mallakin gwamnati wajen farfado da ayyukansu yadda ya kamata, a yayin da suke kokarin kandagarkin yaduwar cutar, domin tabbatar da samar da isassun hajoji, da zaman karko ga kasar. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China