Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a duniya ya zarce 150,000
2020-03-15 20:22:13        cri
Kakakin hukumar lafiya ta duniya WHO, Fadela Chaib, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, baki daya yawan mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a duk duniya ya kai mutane 152,428 ya zuwa safiyar ranar Lahadin nan.

Daga cikin adadin kimanin mutane 5,720 ne suka mutu, tun bayan samun bullar cutar a kasashe da yankunan duniya 141, in ji Chaib. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China