Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya bukaci a ayyana yaki kan cutar COVID-19
2020-03-14 16:36:33        cri
Kwanaki 2 bayan hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cutar COVID-19 a matsayin annobar da ta shafi duniya baki daya, sakatare janar na majalisar, Antonio Guterres, ya bukaci kasashen duniya su ayyana matakin yaki kan cutar.

Antonio Guterres, wanda ya bayyana haka a jiya, ya ce kowa na da hakkin bin shawarar likitoci na kula da lafiya da daukar matakai masu sauki da hukumomin lafiya suka gabatar.

Sakatare janar din ya yi gargadin cewa, duniya na fuskantar barazanar lafiya da ba a taba ganin irinta ba.

Baya ga matsalolin lafiya da suka shafi al'umma, ya ce kwayar cutar na mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya.

Ya ce kasuwannin hada-hadar kudi sun gamu da rashin tabbas, harkar samar da kayayyaki na fuskantar tarnaki, harkokin zuba jari da bukatar kayayyaki sun ragu, inda ake fuskantar hadarin gaske na shiga masassarar tattalin arziki a duniya.

Har ila yau, ya ce dole ne a hada hannu wajen dakile cutar da shawo kan matsalolin da ta haifar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China