Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakaki: Sin ba za ta yi shiru bayan an yi mata wulakanci ba
2020-02-24 20:02:07        cri

Yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin mista Zhao Lijian, ya yi furuci game da wani labari na wulakanta kasar Sin da jaridar "The Wall Street Journal (WSJ)" ta kasar Amurka ta wallafa, inda kakakin ya ce kasar Sin ba za ta yi shiru, game da wannan wulakancin da aka yi mata da gangan ba.

An ce a ranar 20 ga watan da muke ciki ne, wasu ma'aikatan jaridar WSJ 53 dake aiki a kasar Sin, suka yi hadin gwiwa wajen aikewa da wani sako ga shugaban kamfanin jaridar, don bukatar a gyara taken labarin da aka sanya mai ma'anar wulakanta kasar Sin, da neman gafara daga wadanda aka keta hakkinsu ta labarin.

Ma'aikatan sun bayyana a cikin wasikar cewa, "Batun bai shafi ikon edita na zaman kansa ba, kuma bai shafi batun raba tsarin labarai da na bayanan sharhi ba. Saboda taken wannan labari kuskure ne, kuma ya fusata al'ummomi daban daban, ciki har da Sinawa." Amma duk da haka, kakakin jaridar WSJ ta mayar da martani a ranar 22 ga wata, cewar jaridar ba ta canza matsayarta ba.

A nasa bangare mista Zhao Lijian, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da wannan batu, a wajen wani taron manema labarun da ya gudana a yau Litinin, ya ce da farko dai, kasar Sin ba za ta yi shiru ba kan wannan wulakancin da aka yi mata. Sa'an nan na biyu, jaridar WSJ ta ce ayyukan watsa labarai, da wallafa sharhi mabanbantan harkoki ne masu zaman kansu, don haka ba ta da alhaki game da abun da aka rubuta, duk da cewa wannan furuci ba shi da ma'ana ko kadan.

Har ila yau, jami'in ya kalubalanci shugabannin jaridar WSJ da su fito a fili, su nemi gafarar jama'ar kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China