Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan jihar Lagos ya yabawa Sin kan kokarinta wajen yaki da cutar COVID-19
2020-03-04 10:51:26        cri

Gwamnan jihar Lagos ta Nijeriya, Babajide Sanwo-Olu, ya aike da wasiku ga shugaban lardin Guangdong Ma Xingrui da magajin birnin Guangzhou Wen Guohui ta ofishin jakadancin Sin dake jihar, inda ya nuna goyon bayansa ga kasar Sin, ya kuma bayyana cewa, tabbas Sin za ta cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

 

Ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayyukansu sakamakon annobar, yana mai bayyana annobar a matsayin babban kalubalen dake gaban al'ummomin Sin da Nijeirya, da ma dukkanin gamayyar kasa da kasa. Gwamnan ya ce kasar Sin ta ba da gudummawarta ga aikin yaki da annobar, lamarin da ya nuna karfinta na cika alkawari da sauke nauyin dake wuyanta yadda ya kamata. Ya kara da cewa, jihar Lagos tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin domin hana yaduwar annobar baki daya. Cikin wasikunsa, ya kuma yi fatan samarwa lardin Guangdong kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma karfafa mu'amalar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin bangarorin biyu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China