Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Algeria ta samu sabbin mutane 3 da suka kamu da cutar COVID-19
2020-03-04 10:03:33        cri

Ma'aikatar lafiyar kasar Algeriya ta sanar a jiya Talata cewa an samu sabbin mutane 3 da suka kamu da cutar numfashi da COVID-19 a kasar, inda a yanzu yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai mutane takwas.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya ruwaito cewa, ma'aikatar lafiyar kasar ta sanar cewa sabbin mutanen uku da suka kamu da cutar dukkansu daga iyali guda ne cikin mutane hudun da suka kamu da cutar tun da farko a lardin Blida, mai nisan kilomita 50 daga babban birnin kasar Algiers.

Ma'aikatar lafiyar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike game da yaduwar cutar domin gano dukkan mutanen da suka yi mu'amala da mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar.

A ranar 25 ga watan Fabrairu, Algeriya ta sanar da rahoton mutum na farko da ya kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 wato wani mutum dan kasar Italiya wanda ya shiga kasar Algeria a ranar 17 ga watan Fabrairu. Yayin da aka samu karin mutane hudu 'yan gida daya da suka kamu da cutar ta COVID-19 a lardin Blida wanda suka dauki cutar daga jikin wasu iyalai biyu daga kasar Faransa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China