Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin harkokin wajen Sin da Iraki sun tattauna ta wayar tarho kan batun yakar COVID-19
2020-03-10 10:50:05        cri

Mamban majalisar zartaswar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa ministan harkokin wajen Iraki Mohammed al-Hakim a ranar Litinin, inda suka tattauna game da batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wang ya ce, bayan da aka samu barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Iraki, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da shirin tura tawagar jami'an ba da agaji na Red Cross na kasar Sin inda ta tura tawagar jami'an kiwon lafiya zuwa Iraki, bisa imanin cewa tawagar za ta tallafawa Irakin a yaki da take yi da annobar cutar COVID-19 da ta barke, kuma kasar Sin tana da kwarin gwiwa al'ummar Iraki za su samu nasarar kawar da cutar nan bada jimawa ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China