Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jirgin ruwan "Grand Princess" ya tsaya a dab da gabar teku a hukumance
2020-03-10 10:49:20        cri

A jiya Litinin ne, jirgin ruwan "Grand Princess" ya tsaya a tashar ruwa ta Oakland na jihar California na kasar Amurka bayan shafe kwanaki da dama yana watangaririya a kan teku. Wata sanarwar da ofishin kula da harkokin gaggawa na jihar California ya fidda na cewa, tun a jiya an shirya yadda fasinjoji za su fara sauka daga jirgin ruwan, kuma mai iyuwa ne za a shafe kwanaki 2 ko 3 kafin a sauke dukkan fasinjojin. Kana, bisa yadda da gwamnatin ta tsara, za a fara fitar da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19.

Sa'an nan, za a ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar a asibitin dake jihar California, za kuma a kebe wani wuri na musamman don killace fasinjoji 'yan jihar Californai da ba su da alamun cutar a jihar ta California, za kuma a dauki sauran fasinjoji wadanda ba 'yan jihar California ba zuwa sauran jihohi, ciki har da sansanonin soja dake jihar Georgia da jihar Texas don a rika sanya ido a kansu.

Bayan saukar da fasinjojin, jirgin ruwa na "Grand Princess" zai tashi daga tashar jirgin ruwa ta Oakland, inda zai tsaya a yankin teku dake nisa da jihar California. Za a yi bincike da ba da jinya ga ma'aikatan jirgin ruwa guda 1111 dake cikin jirgin ruwan. Gaba daya mutane 3500 ne suke cikin jirgin, ya zuwa yanzu, an tabbatar da mutane 21 dake cikin jirgin sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China