Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a murkushe duk makamai masu guba da aka ajiye ko aka yi watsi da su
2019-11-26 13:33:53        cri
An bude taron kasashen da suka amince da yarjejeniyar hana yaduwar makamai masu guba karo na 24 mai kwanaki 5 a birnin Hague a jiya Litinin. A gun taron, wakilin kasar Sin ya nanata cewa, muhimman ayyukan dake gaban kungiyar hana yaduwar makamai masu guba su ne, murkushe dukkan makamai masu guba da aka ajiye ko aka yi watsi da su ba tare da bata lokaci ba, da ingiza hadin kan kasa da kasa a fannin harhada magungunan zamani da musayar ra'ayi a fannin kimiyya da fasaha.

A jawabin da ya gabatar, Mataimakin ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin, Wang Zhijun ya ce tawagar kwamitin gudanarwa na kungiyar hana yaduwar makamai masu guba, sun kai ziyara wurin na'urar murkushe makamai masu guba da rundunar Japan ta yi watsi da su a Ha'erbaling dake lardin Jilin na kasar Sin, kuma Sin ta yi imanin cewa, wannan ziyara za ta taimakawa bangarori daban-daban ganin irin aikin da Sin take gudanarwa, musamman ma fahimtar muhimmancin wadannan ayyuka. Har ila yau, Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban da su ci gaba da sa ido kan wasu matsalolin dake shafar makamai masu guba da rundunar Japan ta yi watsi da su a kasar. Kana Sin za ta nace ga yarjejeniyar da aka kulla, tare da magance a yi amfani da kungiyar hana makamai masu guba wajen cimma burin siyasar wani yanki, kamata ya yi bangarori daban-daban su kai ga matsaya daya don daidaita bambancin ra'ayinsu bisa yin sulhu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China