Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta karrama wasu maluman Afirka guda uku
2019-10-23 20:41:45        cri
A yau ne kungiyar tarayyar Afirka (AU)ta baiwa wasu malaman Afirka kyautar shiyyar ta farko, saboda rawar da suka taka.

Maluman da kungiyar ta karrama, sun hada da Augusta Lartey-Young daga makarantar sakandaren maza ta Presbytereian dake kasar Ghana, da Erick Ademba na makarantar mata ta Asumbi dake Kenya da kuma Gladys K. daga wata makaranta a kasar Uganda, inda aka ba su takardun shaida da tsabar kudi dala dubu 10 kowanne, a wani biki da aka gudanar a hedkwatar kungiyar dake Addis Ababa,babban birnin kasar Habasha.

An karrama maluman ne, saboda nasarorin da suka cimma, da suka hada da ingancin koyarwa da karfafa halaye na kwarai, tsara ayyuka da shirye-shirye wadanda ke karfafa dabi'u na koyon mu'amala da al'adu da taimakawa dalibai cimma burin da suke fatan cimmawa na dogon zango, ta hanyar shirya shirye-shirye da hukumomin da suka dace gami da samar da muhimman bayanai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China