Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta tura dakaru zuwa yankunan dake fama da rikici wadanda ke da rinjayen masu amfanin da Ingilishi, gabanin babban zaben kasar
2020-01-08 10:38:50        cri
Kamaru ta tura jami'an tsaro zuwa yankunan kasar biyu masu fama da rikici, na arewa maso yamma da kudu masu yamma, wadanda ke da rinjayen masu amfani da Ingilishi, domin tabbatar da tsaro gabanin babban zaben kasar da za a yi a watan Febreru.

Kwamandan soji a kasar, Colonel Henry Nchinda, ya shaidawa manema labarai a Buea, babban birnin yankin kudu maso yammacin kasar cewa, za a tura jami'an tsaro dukkan sassan yankunan 2 domin tabbatar da gudanar zabe lami lafiya.

Kwamandan ya bayyana haka ne, bayan wata runduna mai sojoji 350 ta isa yankin kudu maso yammacin kasar.

Colonel Nchinda, Ya ce wadannan jami'an sun je yankin ne domin tabbatar da an gudanar da zabuka cikin yanayi mai aminci.

Za a gudanar da zaben 'yan majalisa da na yankunan Kamaru ne a ranar 9 ga watan Faburairu, duk da barazanar da 'yan aware suka yi. A ranar Juma'a ne, shugabannin 'yan awaren, suka ce za su rufe yankunan na tsawon raneku 6, daga ranar 7 zuwa ranar 12 ga watan Faburairu, a wani yunkuri na hana zabuka gudana a yankunan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China