Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An ba da rahoton sabbin mutane 19 da suka kamu da COVID-19 a babban yankin kasar Sin
2020-03-10 10:16:56        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar a yau Talata, ta samu rahoton sabbin mutane 19 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 da kuma mutane 17 da cutar ta halaka jiya Litinin a babban yankin kasar Sin.

A cewar hukumar, mutane 17 din da suka mutu dukkansu a lardin Hubei ne.

Haka kuma a jiyan, an sallami mutane 1,297 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, yayin da adadin wadanda ke cikin matsanancin hali ya ragu daga 4,794 zuwa 317.

Ya zuwa jiya Litinin, baki dayan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin, ya kai 80,754 ciki har da marasa lafiya 17,721 wadanda ke ci gaba da karbar magani, yayin da aka sallami mutane 59,897 bayan da suka warke daga cutar, sai kuma mutane 3,136 da cutar ta halaka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China