Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta samar da tallafin kudi har dala miliyan 20 ga WHO
2020-03-09 20:33:16        cri
A yau Litinin a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin samar da tallafin kudi da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 20, ga hukumar lafiya ta duniya wato WHO, domin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma taimakawa kasashe masu tasowa, wajen tsara manufofin kiyaye lafiyar jama'a, kana kasar Sin za ta ci gaba da hada kai tare da sauran kasashen duniya, ta yadda za a cimma burin ganin bayan annobar ba da jimawa ba.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi, Geng Shuang ya kara da cewa, makasudin samar da tallafin kudin, shi ne nuna goyon baya ga hukumar lafiya ta duniya, ta yadda za ta kara taka rawa, a aikin dakile annobar da ke bazuwa a fadin duniya, musamman ma wajen taimakawa wasu kasashe masu tasowa, wadanda ke shan wahalar fama da annobar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China