Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta soki Pompeo saboda kiran COVID-19 da ya yi da kwayar cutar Wuhan
2020-03-09 20:31:44        cri
A Litinin din nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya soki sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, bayan da Mr. Pompeon ya kira COVID-19 da kwayar cutar Wuhan.

Yayin taron ganawa da manema labarai da ya gudana a yau, Geng Shuang ya ce, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta riga ta nadawa kwayar cutar numfashin dake bazuwa a fadin duniya sunan COVID-19, amma wasu 'yan siyasar Amurka sun yi watsi da batun kimiyya, kuma ba sa yin biyayya ga kudurin hukumar lafiya ta duniya, inda har ma suke shafawa kasar Sin, da birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar kashin kaji, ta hanyar yin amfani da kwayar cutar, hakika muna adawa da wannan yunkuri da kakkausar murya.

Rahotanni sun nuna cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Pompeo, ya shaidawa manema labarai cewa, dalilin da ya sa Amurka ba ta dakile annobar a kan lokaci ba, shi ne domin kasar Sin ba ta samar da bayanai a fili ba. Kan wannan, Geng Shuang ya jaddada cewa, tun bayan barkewar annobar, nan take kasar Sin ta samar da bayanan da ta tattara ga hukumar lafiya ta duniya, da kasashe da yankunan da abun ya shafa, ciki har da Amurka, lamarin da ya taimaka musu wajen kandagarkin annobar matuka, don haka ba zai yiwu zargin Pompeo ya samu amincewa daga al'ummomin kasa da kasa ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China