Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa sun bayar da gudunmowar sama da yuan biliyan 29 domin yaki da COVID-19
2020-03-09 15:16:42        cri
Kungiyoyin ayyukan bada agaji na kasar Sin da kungiyar Red Cross sun amshi gudunmowar yuan biliyan 29.29 kwatankwacin dala biliyan 4.23 da kayayyakin aikin lafiya miliyan 522 domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ya zuwa ranar Lahadi, wani babban jami'i ne ya tabbatar da hakan a yau Litinin.

Daga cikin gudunmowar, yuan biliyan 23.98 da kayayyaki miliyan 466 an riga an isar da su ga masu bukata bisa ga kokarin da kungiyoyin aikin agajin suka yi, a cewar Zhan Chengfu, mataimakin ministan ma'aikatar kula da jin dadin al'umma, kamar yadda ya bayyanawa taron 'yan jaridu a birnin Beijing.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China