Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kara inganta matakan kare lafiyar ma'aikata 'yan ci-rani daga COVID-19
2020-03-09 11:53:53        cri
A yayin da ake tsaka da kokarin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, hukumomi a kasar Sin sun kara inganta hidimomi na kiwon lafiya ga ma'aikata 'yanci-rani, don kara fadakar da su, da ma kare su daga cutar.

Jami'i a hukumar lafiya ta kasar Yang Wenzhuang shi ne ya bayyana haka, yana mai cewa, yayin da kasar ta Sin ta ke shirya jigilar dawo da ma'aikata 'yanci-rani bakin ayyukansu, a hannu guda kuma za a dauki jerin matakai, ciki har da auna yanayin zafin jiki kafin a fara dawo da su.

A cewarsa, ba za a bar marasa lafiya da suka harbu da cutar, da wadanda ake zaton sun kamu da cutar da wadanda suka mu'amala da su, da masu alamomi na zazzabi su dawo ba. Haka kuma, za a tsara ma'aikata 'yanci-rani da suka dawo bakin aiki bisa yanayin matakan hadarin cutar a yankuna daban-daban na kasar. Ya kuma jaddada cewa, ma'aikatan ba za su biya kudin takardar shaidar lafiya ko gwaje-gwaje da wasu kudade ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China