Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Burkina Faso ta tabbatar da rahoton mutane biyu sun kamu da cutar COVID-19 a karon farko
2020-03-10 09:42:49        cri

Ministan lafiyar kasar Burkina Faso Claudine Louge ya sanar a jiya Litinin a taron manema labarai cewa mutane biyu sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a karon farko a kasar.

A cewar Louge, mutanen biyu ma'aurata ne inda matar ta dawo daga kasar Faransa a kwanan nan. A yanzu haka an killace majinyatan a wani asibiti dake Ouagadougou, babban birnin kasar.

Mutum na uku wanda shi ne ya yi mu'amala da mutanen biyu da suka kamu da cutar ana ci gaba da bibiyarsa, a cewar ministan lafiyar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China